Firaministan kasar Mali, Diango Cissoko ya nuna jin dadinsa a ranar Talata a birnin Banamba mai tazarar kilomita 140 daga Bamako, babban birnin kasar dake yankin Koulikoro, inda aka ajiye sojojin Najeriya, ga masu shiga tsakani biyu kan rikicin kasar Mali, wato shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan da shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore da shugaban kungiyar ECOWAS, kuma shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Dramane Ouattara.
Babban jami'in gwamnatin kasar Mali ya kai ziyara a Banamba domin nuna jinjinawa ga tawagar sojojin Najeriya, inda ya nuna yabo kan sanin ya kamata na wadannan sojoji da nan da nan suka saba da yanayin wurin haka kuma sojojin Najeriya suna mu'amala yadda ya kamata tare da al'ummomi, hukumomi da kuma 'yan siyasa da suka hada da gwamnan yankin Koulikoro, babban magajin gari da karamin magajin gari.
Mista Cissoko ya nuna godiya a madadin shugaban kasar Mali forfesa Dioncounda Traore, hukumomin gwamnati da kuma al'ummar Mali ga rukunin tawagar MISMA dake Banamba, ga tawagar MISMA da kuma kungiyar ECOWAS tare da shugabanta Alassane Dramane Ouattara. (Maman ADA)