Uwar gidan shugaban kasar Mali na wucin gadi, madam Mintou Doucoure dake ziyarar aiki a kasar Amurka, ta nemi taimako daga masu hannu da shuni domin sake gina kasar Mali bayan yaki da dawowar wadanda aka kaura da su da 'yan gudun hijira na yankunan arewacin kasar Mali, in ji wani labarin da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samu daga hukumomin kasar.
Taron Afrika karo na biyu kan batun kiwon lafiya na matan shugabanni ya bude ranar Talata a zauren kasa da kasa na Los Angeles, a cikin jihar California ta kasar Amurka, a cewar wata sanarwa ta ofishin matar shugaban kasar dake birnin Bamako.
Dandali dake karkashin jagorancin manyan likitocin Amurka dake taimakawa Afrika, tare da taimakon cibiyar MDD kan dangantaka da hadin gwiwar kasashen Afrika, ya samu halartar kimanin matan shugabannin kasashen Afrika goma.
A cikin jawabinta, madam Mintou Doucoure ta mai da hankali kan manyan kalubalolin kiwon lafiya da suka hada da yaki da ciwon sida, daukar nauyin mutanen dake dauke da kwayoyin wannan cuta, yaki da malaria, rage mutuwar kananan yara, yaki da ciwon shan inna da sauransu.
Haka kuma madam Mintou Doucoure ta yi amfani da wannan dama domin yin kira da a taimakawa miliyoyin mata, yara da tsofafin da aka tilastawa yin gudun hijira zuwa kasashe makwabta ko a