in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Faransa da Cote d'Ivoire sun yaba da kafa kwamitin sasanta 'yan kasa a Mali
2013-04-12 10:50:12 cri

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande da takwaransa na kasar Cote d'Ivoire, Alassane Dramane Ouattara sun yaba a ranar Alhamis a birnin Paris, da kafa kwamitin sasanta 'yan kasa da zai gudanar da muhimmin aikin taimakawa maido da hadin kai da zaman lafiya a kasar Mali, a wata sanarwar fadar Elsyee da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kofi.

Francois Hollande ya gana da Alassane Dramane Ouattara, shugaban kasar Cote d'Ivoire a ranar Alhamis. Shugabannin biyu sun tabo rikicin kasar Mali tare da cimma matsaya guda na yin aiki tukuru domin ganin an tsai da jadawalin zabubuka.

Kungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWAS da kasar Cote d'Ivoire take shugabanta a wannan karo, za ta cigaba da kokarin taimakawa Mali bisa la'akari da shiga tsakanin kasar Burkina Faso.

Haka kuma shugabannin biyu sun tabo batun cigaban da aka samu kan shawarwarin kwamitin sulhu a birnin New York kan mai da tawagar taimakawa Mali ta kasa da kasa (MISMA) a karkashin jagorancin Afrika dake aikin tabbatar da zaman lafiya da sunan MDD.

A ranar 28 ga watan Maris, mista Hollande ya nuna fatansa na ganin an gudanar da zabubuka a karshen watan Yuli, da batun janye sojojin Faransa daga kasar Mali. Sojojin Faransa 2000 kadai za su kasance a kasar Mali a cikin watan Yulin shekarar 2013 bisa 4000 a halin yanzu. Kuma za'a fara janye a karshen watan Afrilun da muke ciki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China