in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nada sabon jakadan Faransa a Mali
2013-03-22 10:43:36 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa ta tabbatar da nadin sabon jakadan kasar da za a tura kasar Mali, daidai gabar da kasar ke ci gaba da taimakawa matakan soji a Malin.

Sabon jakadan mai suna Gilles Huberson, wanda tsohon mashawarci kan harkokin kasashen waje ne, zai maye gurbin Christian Rouyer, wanda ke rike wannan mukami tun cikin watan Maris na shekarar 2011. A cewar mai magana da yawun ma'aikatar Philippe Lalliot, wannan canji ya biyo bayan sauye-sauyen da ake yiwa ofisoshin jakadancin kasar ta Faransa dake nahiyar Afirka ne. Lalliot ya kara da cewa, tuni ma'aikatar ta mika sunan Mr. Jean Felix Paganon ga mahukunta, domin nada shi jakadan kasar a Senegal.

Sai dai wasu rahotanni daga Malin sun ce, an samu sabani tsakanin tsohon jakadan kasar, da ministan harkokin wajen Faransan Laurent Fabius, duk kuwa da kasancewar jakadan na goyon bayan ayyukan soji da Faransan ke aiwatarwa a kasar ta Mali.

Kasar Faransa dai na da tarin sojoji da yawansu ya kai 4,000 a kasar ta Mali. A ranar Larabar da ta gabata, shugaba Francois Hollande na Faransan ya bayyana cewa, nan da 'dan lokaci, kusan daukacin yankunan kasar Malin za su komo karkashin ikon mahukuntanta, yayin da shi kuwa firaministan kasar Jean-Marc Ayrault, ya bayyana wa majalisar dokokin kasarsa cewa, nan da karshen watan Afrilu mai zuwa, sojojin kasar za su fara komawa gida.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China