Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana a ranar Alhamis da yamma bisa kafar France 2 cewa, sojojin kasarsa ba za su wuce 2000 ba a kasar Mali a cikin wata Yuli mai zuwa.
A yayin wata hira a tashar talabijin ta France 2, shugaban kasar Faransa ya jaddada cewa, mun cimma burin da muka sanya a gabanmu na dakatar yunkurin 'yan ta'adda da kuma karbe biranen dake hannnunsu.
Haka kuma shugaba Hollande ya nuna fatansa na ganin an shirya zabubuka a kasar Mali kafin karshen watan Yuli tare da fatan ganin dukkan makarraban jama'ar kasar Mali su sami wakilci a wadannan zabubuka. (Maman Ada)