in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaki na kara tsananta a garin Gao na kasar Mali
2013-03-25 10:58:22 cri

Yaki na kara tsananta yanzu haka tsakanin 'yan ta'adda da rundunar sojojin kasar Mali tare da kawayenta a cikin garin Gao.

'Muna cikin tsaka mai wuya, 'yan ta'adda sun shigo gari, daga baya kuma suka fara kai hare-hare tun jiya a unguwar Chateau dake bisa hanyar fita daga gabashin garin mai tazarar kilomita uku da sansanin soja na 2 da kuma filin saukar jiragen sama inda sojojin kasar Faransa suke. Suna da yawa sosai, duk da haka mun samu gusasu, amma kuma sun koma unguwa ta hudu, a yankin dake fita zuwa Kidal.' in ji wani ofisa na sojojin Mali da aka tuntuba ta wayar tarho a ranar Lahadi.

Jami'in sojan ya bayyana cewa, wani sojan kasar Mali ya mutu a cikin wata musanyar wuta. Harin na garin Gao ya biyo bayan wani karin mayaka da kayayyaki da kungiyar MNLA ta samu a ranar 20 ga watan Maris da suka fito daga kasar Libiya.

Haka kuma bayyanai sun ce, an gano wani tsohon kanal na rundunar sojojin kasar Mali, Mbareck Ag Akly tare da wasu mayaka kusan dari bisa tsaunukan Taikarene a cikin yankin Menaka kilomita 300 daga Gao a ranar 22 ga watan Maris. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China