in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan motoci da Sin ta kera ta kuma sayar, dukkansu sun kai fiye da miliyan 5 cikin farkon watanni uku na wannan shekara
2013-04-15 15:26:54 cri

An kago matsayin koli a watan Maris na bana a fannin kera da kuma sayar da motoci a kasar Sin, sabo da haka yawan motocin da aka kera da kuma sayar a watanni uku na farkon wannan shekara ya fi adadin da aka zata tun da farko.

Kungiyar masana'antar kera motoci ta kasar Sin ta gabatar da wata kididdiga a ran 11 ga wata cewa, a cikin farkon watanni uku na bana da suka gabata, yawan motoci da aka kera ya kai miliyan 5 da budu 397.1, wanda hakan ya nuna karuwar kashi 12.8 cikin dari, bisa na makamancin lokaci na bara, yayin da kuma yawan wadanda aka sayar ya kai miliyan 5 da dubu 424.5, adadin kuma ya karu da kashi 13.2 cikin dari, bisa na makamancin lokaci na bara. Matakin da ya ba da alamu masu nuna cewa, wannan sha'ani zai ci gaba da samun bunkasuwa a nan gaba.

Watan Maris wata ne mai kyau wajen kera da kuma sayar da motoci, adadinsu ya kai sabon matsayi a tarihi. Daga cikin wannan adadi, motocin daukar fasinjoji sun samu bunkasuwa da sauri, hakan ya zama babban karfin bunkasa sha'anin hada-hadar motoci a kasar ta Sin. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China