in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan motocin da Sin ta kera kuma ta sayar a shekarar 2012 ya kai matsayi na farko a duniya
2013-02-05 16:08:16 cri
Bisa labarin da ma'aikatar kula da harkokin masana'antu da sadarwa ta kasar Sin ta bayar kwanan baya a shafinta na intanet, an ce, a shekara ta 2012, kasuwannin motocin kasar Sin sun ci gaba da samun bunkasuwa, har matsakaicin yawan motocin da aka fitar a kowane wata ya haura miliyan 1.5, gaba daya adadin da aka fitar cikin shekarar 2012 ya haura miliyan 19, wanda ya kai wani sabon matsayi a tarihin duk duniya.

Bugu da kari, bisa kididdigar da kungiyar masana'antar kera motoci ta Sin ta yi, an ce adadin motoci da Sin ta kera ya kai miliyan 19 da dubu 271.8 a shekarar da ta wuce, adadin ya karu da kashi 4.6 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2011, haka nan kuma yawan motoci da aka sayar ya kai miliyan 19 da dubu 306.4, adadin ya karu da kashi 4.3cikin dari bisa na shekarar 2011. (Maryam).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China