in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cinikin motoci ta kasar Sin zai samu bunkasuwa na lokaci mai tsawo
2012-02-07 16:50:07 cri

Kwanan baya, kungiyar masana'antun motoci ta kasar Sin ta ba da labari cewa, yawan motocin da Sin za ta samar cikin wannan shekara zai kai kimanin miliyan 20 wanda zai karu da kashi 8 bisa 100. Hakan ya sa, cinikin motoci ta kasar Sin zai samu bunkasuwa cikin lokaci mai tsawo.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, yawan motoci da ba sa fitar da gurbatacciyar iska da yawa ba, da za a sayar zai wuce miliyan 10 wanda zai karu da kashi 5 bisa 100.Haka kuma yawan motocin da za a sayar domin kasuwanci zai kai miliyan 4 wanda zai karu da kashi 2 bisa 100.

Ban da wannan kuma, karfin yin kokawa na kasar Sin a wannan fanni na cinikin motoci ya karu sosai, an yi kiyasin cewa, yawan motocin da Sin za ta fitar cikin wannan shekara zai kai daga miliyan 1.05 zuwa miliyan 1.1 wanda zai karu daga kashi 25 zuwa 30 cikin 100 bisa na shekarar bara.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China