Wan Gang ya bayyana cewa, a cikin dalilan da suka gurbata iskar manyan biranen kasar Sin a halin yanzu, kashi 70 cikin kashi dari shi ne gurbatacciyar iska da motoci suka fitar. A matsayinta ta kasa mafi girma wajen samar da kuma sayen motoci a duniya, tabbas ne kasar Sin ta bi wata hanyar raya masana'antun motoci bisa sabbin makamashi, wato kera motoci masu amfani da wutar lantarki.
Bugu da kari kuma Wan Gang ya ce, idan ana son yada motoci masu amfani da wutar lantarki da sauran sabbin makamashi, to zirga-zirgar jama'a za ta kasance wani fanni mafi muhimmanci.(Kande Gao)