in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta samu sakamako mai kyau wajen rage gurbatacciyar iska da motoci suke fitarwa
2011-12-20 16:35:44 cri

Ma'aikatar kiyaye muhalli ta kasar Sin ta sanar a ran 19 ga wata a nan birnin Beijing cewa, cikin shekaru 5 da suka wuce, yawan motocin kasar Sin ya karu da kashi 150 cikin dari, amma yawan gurbatacciyar iskar da suka fitar ya karu da kashi 7.4 cikin dari ne kawai.

Kakakin ma'aikatar kiyaye muhalli ta kasar Sin Tao Detian ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta kara karfin rage gurbatacciyar iskar da motoci suke fitarwa, wato ta tsaurara matakan shigo da sabbin motoci da yin amfani da makamashi mai tsabta da yin watsi da motocin da suka fi gurbata muhalli da sauransu, wannan ya sa, kasar Sin ta samu sakamako mai kyau wajen hana karuwar yawan gurbatacciyar iskar da motoci suke fitarwa.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China