Bisa labarin da aka bayar, an ce, daga shekarar 2011, za a fara gudanar da shirin bunkasuwa a karo na 12 na shekaru biyar-biyar a sana'ar kera motoci, kuma an jaddada cewa, za a bunkasa sana'ar kera motoci don ta zama sahun gaba a duniya, haka kuma an bayyana cewa,yawan motocin da ake sayarwa zai ci gaba da karuwa.
Kwararru sun bayyana cewa, bayan da sana'ar motoci ta zama sahon gaba a duniya, sana'ar motoci a kasar Sin za ta zama wani muhimmin abu ne a cikin tsarin sana'ar motoci na duniya.(Bako)