Mahukunta a Najeriya sun ce, an tsamo gawawwakin jami'an rundunar 'yan sanda 10 cikin 12, da aka tabbatar wasu 'yan bindiga sun hallaka, a jihar Bayelsa dake kudancin kasar.
Wata sanarwa da ta fito daga rundunar 'yan sandan kasar, ta tabbatar da mika gawawwakin 'yan sandan ga dakin ajiya dake asibitin birnin Yenagoa, kuma ko da yake an hana manema labaru shiga dakin da aka ajiye matattun 10, wata majiyar 'yan sanda ta tabbatar da adadin wadanda aka gano din.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai, kungiyar tsagerun Niger Delta da aka fi sani da MEND, ta ayyana kisan 'yan sanda sama da 15, bayan sun yi musu kwantan-bauna a garin Azuzama, yayin da suke kan hanyarsu ta halartar wani taro, sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta ce, jami'an ta 12 ne suka rasu, yayin dauki ba dadin da ya auku tsakaninsu da tsagerun na MEND. Wannan farmaki dai shi ne mafi kazamta a yankin na kudu maso kudancin Najeriya, tun bayan da kungiyar, ta kuduri aniyar sake daukar makamai, biyowa bayan hukuncin dauri da aka yankewa daya daga 'ya'yanta Henry Okah a kasar Afirka ta Kudu, bisa zarginsa da aikata laifukan ta'addanci, matakin da kungiyar tasa ta MEND ta ce sam ba za ta lamunta ba.(Saminu)