Mahukuntan sojin kasar Najeriya sun sanar ranar Laraba cewa, an kashe a kalla mutane hudu shekaran jiya wadanda ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne a arewa maso gabashin kasar dake yankin Afirka ta yamma.
Dakarun na Najeriya sun harbe 'yan bindigan ne ranar Talata da yamma bayan musayar wuta a garin Geidam dake da nisan kilomita 180 daga Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Mai magana da yawun rundunar soji ta JTF a jihar Yobe, Lt Eli Lazarus ya tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa, inda ya ce, an yi musayar wuta ne tsakanin sojoji da 'yan bindigar da misalin karfe biyar na yamma ranar Talata.
Ya ci gaba da cewa, lamarin ya auku ne lokacin da wadanda ake kyautata zaton 'yan ta'adda ne suka kawo hari kan jami'an tsaro na JTF dake garin Geidam, inda sojojin suka cimma nasarar shawo karfin harin, har suka kashe 'yan bindiga guda hudu.
An gano bindigogi kirar AK47 guda uku, da albarusai daga hannun 'yan tawayen.
Eli Lazarus ya ba da tabbaci ga jama'a cewa, hukumar tsaro ta JTF ta sha damarar maido da zaman lafiya da oda a yankin da kuma tabbatar da doka da oda.
Jihar Yobe dai na cikin wurare da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi katutu, tun bayan da kungiyar ta fara kai hari a shekarar 2009.(Lami)