Rundunar 'yan sanda a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Nigeria, ta tabbatar da rasuwar mutane 25, sakamakon wani harin da wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai suka kai wa wasu wurare 13 a karamar hukumar Ganye, dake jihar ta Adamawa a ranar Juma'ar da ta gabata.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Mohammed Ibrahim ya bayyanawa manema labaru cewa, mataimakin babban jami'in gidan yarin na garin Ganye Malam Buba Musa, da wani jami'in 'yan sanda guda, na cikin wadanda suka rasu yayin harin. Shi ma babban jami'in gidan yarin na jihar ta Adamawa Andrew Barka, ya tabbatar da rasuwar abokin aikin nasa, ya kuma kara da cewa, maharan sun baiwa tsararru 127 damar arcewa daga gidan yarin, ko da yake ya ce, suna ci gaba da daukar matakan tsafke dukkanin wadanda suka gudu yayin harin.
Ya zuwa ranar Lahadi dai ba a kama ko da mutum guda dake da alaka da harin ba. Kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua dai ya rawaito yadda wannan balahira ta auku a garin na Ganye a ranar Juma'ar da ta gabata, inda shaidun gani da ido suka bayyana kaiwa wasu wurare hari, ciki hadda bankin garin, da ofishin 'yan sanda da kuma gidan yari.(Saminu)