in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar tsageru ta MEND a Nigeria ta ce ta hallaka jami'an tsaro 15
2013-04-08 10:37:00 cri

Wata sanarwa daga kungiyar tsageru ta yankin Niger Delta a Nigeria, wadda aka fi sani da MEND, ta ce, dakarun kungiyar sun kashe wasu jami'an tsaro 15, yayin wani dauki-ba-dadi da ya gudana a yankin Azuzama, dake kudancin jihar Bayelsa a ranar Juma'ar da ta gabata.

Wannan dai kwantan-bauna da ya janyo salwantar rayukan jami'an 'yan sanda da dama, shi ne irinsa na farko a baya-bayan nan, ya kuma zo ne bayan da kungiyar tsagerun ta ambata cewa, za ta ci gaba da kai hare-hare ga muradun gwamnatin kasar, a wani mataki na ramuwar gayya, don gane da hukuncin dauri da aka yankewa daya daga cikin 'yayanta mai suna Henry Okah a kasar Afirka ta Kudu.

Sanarwar da kakakin kungiyar ta MEND Jomo Gbomo ya rabawa manema labaru, ta bayyana cewa, sun dauki wannan mataki ne domin nunawa gwamnatin da gaske suke yi, don gane da kashedin da suka gabatar a baya. Gbomo ya yi fatan hakan zai zamo darasi ga rundunar jami'an tsaron hadin gwiwa ta JTF, da a cewarsa ke furta kalamai marasa tushe, don gane da barazanar da MEND din ta yi.

Sai dai a nata bangare, rundunar 'yan sandan jihar ta Bayelsa, a bakin kwamishinanta Kingsley Omire, cewa ta yi, 'yan sanda 12 ne aka tabbatar da rasuwarsu a harin na ranar Juma'a. Omire ya ce, tuni aka aika da masu aikin ceto, domin tsamo gawawwakin wadanda aka hallaka.

Kwamishinan ya bayyana takaicin yadda aka hallaka jami'an da ba su ji ba ba su gani ba. A ranar Larabar da ta gabata ne dai, kungiyar tsagerun ta MEND ta yi barazanar sake komawa yakin sunkuru da a baya take gudanarwa a wannan yanki mai arzikin man fetur, inda ta sha kai hare-hare kan bututun mai mallakar kamfanonin hakar man dake yankin, tare da ragowar ayyukan ta'adda, da suka hada da garkuwa da ma'aikatan kamfanonin, da lalata kayayyakin aikin da kamfanonin ke amfani da su.

Tsakanin shekarar 2006 kawo yanzu dai, kungiyar ta yi garkuwa da ma'aikatan da yawansu ya kai 400, wadanda suka kubuta bayan an biya kudaden fansa a kansu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China