in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun kashe wani da ake zargi 'dan kungiyar Boko Haram
2013-04-04 10:08:55 cri

Jami'an tsaro a kasar Najeriya na hukumar hadin gwiwa ta JTF sun kashe wani 'dan bindiga ranar Laraba a jihar Kano dake arewa maso yammacin kasar yayin sumame da suka kai a gidan 'dan bindigar wanda suke kyautata zaton 'dan kungiyar Boko Haram ne.

Mai magana da yawun hukumar tsaron lieutenant Ikedichi Iweha ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua inda ya kara da cewa, an cafke wani 'dan bindiga daban yayin sumamen.

Wakilin Xinhua a jihar ya ce, jami'an tsaro sun yi wa mafi yawan sassan birnin kawanya tare da karin cewa, an ji karar bindiga yayin sumamen da aka shafe awa guda ana yi.

Ana yawan samun kai hare-hare a jihar Kano, wacce ita ce ta fi yawan jama'a a arewacin Najeriya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China