in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'yan sanda a Nigeria ta gano wasu makamai a wata maboya dake Kano
2013-03-28 10:37:56 cri

Rundunar 'yan sandan Nigeria ta bayyana cewa, ta yi nasarar gano wata maboyar muggan makamai, da suka hada da na'urar harba bom, da tarin harsasai, da kuma wata mota kirar Golf, a kauyen Inusawa dake karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano.

A cewar kwamishinan rundunar na jihar ta Kano Musa Daura, hakan ya biyo bayan rahoton sirri da suka samu. Wannan dai lamari ya zo daf da lokacin da rundunar ke dada tsaurara matakan tsaro, gabanin bukukuwan Ista, na mabiya addinin Kirista dake tafe.

Da yake tabbatarwa kamfanin dillanci labarai na kasar Sin Xinhua aukuwar wannan lamari, Daura ya kara da cewa, masu motar da aka yiwa tsinke yayin binciken, sun bude wa tawagar 'yan sandan wuta, inda nan take jami'an tsaron suka mai da martani, lamarin da ya sanya maharan arcewa da raunukan bindiga.

Ya ce, motar da 'yan bindigar suka bari na dauke da tarin bindigogi, da albarusai, da kuma wasu jarkokin mai, masu kunshe da ababen fashewa, da kananan gurneti, da kuma na'urorin sarrafa ababen fashewar da dama.

Wannan dai simame da rundunar jami'an tsaron ta yi a jihar ta Kano, ya zo kasa da kwanaki goma da kai wani mummunan hari kan wata motar safa ta fasinja, wadda ke kokarin tashi zuwa jihar Lagos daga tashar motoci ta Sabon Gari dake jihar. Lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 22, yayin da kuma wasu 65 suka jikkata.

An dai sha kai hare-hare a jihar ta Kano dake arewacin kasar mai yawan al'umma, wadda kuma ke kunshe da mabiya addinin Kirista masu dama.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China