Mahukuntan jihar Abia, daya daga jahohin Nigeria masu arzikin man fetur, sun bukaci dukkanin kamfanoni masu zuba jari a fannin man fetur da iskar gas, da su shiga a dama da su, a hada-hadar arzikin da jihar ke tinkaho da shi.
Kwamishinan albarkatun man fetur na jihar Don Ubani ne ya yi wannan kira a garin Umuahia ranar Lahadi 7 ga watan nan, yana mai cewa, gwamnati ta samar da dukkanin kyakkyawan yanayi, da masu zuba jari za su bukata a jihar. A cewar kwamishinan, wannan kira ya zama wajibi, domin rage kaka-gidan da kamfanin Shell ya yi a harkokin da suka shafi hada-hadar man na fetur a jihar.
Daga nan sai Ubani ya bayyana mamakin yadda kamfanoni da dama da a baya suka nuna sha'awar mu'amala da jihar ta wannan fage, ke janye jikinsu cikin 'dan lokaci, musamman duba da irin tarin ribar da za su iya samu, idan sun shiga an dama da su. Har ila yau kwamishinan ya ce, akwai ma karin filayen hakar mai da har yanzu, ba a fara aiki a kan su ba, don haka ya ce, idan har kamfanin Shell da tuni yake gudanar da ayyukansa, ba shi da sha'awar fadada aikinsa zuwa wadannan filaye, hakan dama ce ga ragowar kamfanoni da ba su rigaya sun shiga jihar ba.(Saminu)