A kalla mutane 28 ne jami'an tsaron jihar Plateau dake tsakiya maso arewacin Najeriya suka tabbatar da mutuwarsu a ranar Talata, bayan da wasu mutane masu dauke da makamai suka kai hari kan wasu mazauna wannan jihar.
Komishinan 'yan sanda Chris Olakpe ya shedawa manema labarai a Jos, hedkwatar jihar Plateau cewa, wani 'dan sanda ya jikkata yayin wannan harin na kauyen Ganwuri a cikin karamar hukumar Riyom ta jihar.
Kuma mista Olakpe ne ya gano gawar Kaporal Maniru Jibril, 'dan sandan da ya mutu a cikin wannan hari.
Ko da yake har yanzu ba'a san mutanen da suka kai wannan hari su waye ba, amma duk da haka, ana cigaba da nemansu ruwa jallo, in ji jami'in na 'yan sandar.
Wannan hari ya faru mako guda bayan wani hari makamancin haka da aka kai a kauyen Mavo dake cikin karamar hukumar Wase ta jihar wanda ya haddasa mutuwar mutane 10. (Maman Ada)