in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya lashi takwabin daurewar nasarar da aka cimma game da cutar kanjamau
2012-12-02 19:22:20 cri
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa zai tabbatar da daurewar nasarorin da aka cimma wajen yaki da cutar kanjamau a kasar.

Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a wani zama na musamman don bikin ranar yaki da cutar kanjamau na duniya na shekara 2012, da aka gudanar a Abuja, yana mai cewa, gwamnati tana da kudiri a siyasance na aiwatar da hakan.

A cewarsa, gwamnati na la'akari da cewa, cutar kanjamau babbar barazana ce ga ci gaba mai daurewa kuma ana bukatar makuden kudaden domin a kawar da wannan annoba.

Shugaban ya shaidawa mahalarta taron cewa, hadin gwiwar matakan da aka yi da gwamnatin Amurka a shekara ta 2001, zai kai ga karin kashe kudade kan yaki da cutar daga kashi 25 cikin 100 a halin yanzu zuwa kashi 50 cikin 100 a shekara ta 2015.

Ya ce rahoton MDD game da cutar HIV da rahoton AIDS, sun nuna cewa, an samu gagarumin ci gaba a duniya baki daya a kokarin da ake na kawar da sabbin masu kamuwa da cutar, nuna wariya da masu dauke da cutar da kuma kawar da wadanda ke mutuwa sanadiyar cutar.

Shugaba Jonathan ya kuma bayyana cewa, rahoton ya nuna kudurin shugabannin Afirka na shiga tsakani ta hanyar karin zuba jari kan matakan yaki da cutar a kasahen Afirka da ke kudu da hamadar sahara. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China