in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka kamu da cutar kanjamau ya ragu a Kamaru
2012-03-22 15:21:37 cri
Kwanan baya, bisa wani rahoto kan bincike da ma'aikatar kula da harkokin kiwon lafiya ta kasar Kamaru ta bayar, an ce, a shekarar 2011, yawan mutanen da suka kamu da cutar kanjamau ya ragu zuwa kashi 4.3 cikin 100, kuma abin da ya yi kasa da yawan adadi na shekarar 2010 wato kashi 5.1 cikin 100.

Haka kuma, binciken ya nuna cewa, a shekarar 2011, yawan maza da suka kamu da cutar kanjamau ya kai kashi 2.9 cikin 100, yayin da wannan adadi ya kai kashi 5.6 cikin 100 ga matan kasar. Amma a shekarar 2010, yawan maza da suka kamu da cutar ya kai kashi 4.1 cikin 100, yayin da adadin ya kai kashi 6.8 cikin 100 ga matan kasar.

Ban da wannan kuma, wani jami'in kwamitin yaki da cutar kanjamau na kasar Kamaru ya bayyana cewa, raguwar yawan mutanen da suka kamu da cutar ya dangane da kokari na kasashen duniya da na gwamnatin kasar Kamaru.

A cikin 'yan shekarun nan, Kamaru ta inganta ilmantar da jama'a wajen yaki da cutar kanjamau, kuma sun dauki matakai da dama a game da aikin jinya kyauta ga wadanda suka kamu da cutar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China