in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu da wani kamfanin kasar Switzerland za su fitar da maganin cutar sida mai rahusa
2012-02-11 17:38:25 cri
Gwamnatin Afrika ta Kudu a jiya jumma'a 10 ga wata ta kaddamar da wani shiri tare da wani kamfanin kasar switzerland don sarrafa maganin cutar sida.

Ita dai wannan shiri an yi shine don rage tsadar maganin da ke magance cutar ta sida wato HIV/AIDS, kamar yadda Ministar kimiyya da fasaha na kasar Afrika ta kudu Naledi Pandor ta ce, "wannan shirin na hadin gwiwa mai suna Ketlaphela zai kafa masana'antar samar da maganin na farko wanda zai samar da abubuwan da ake bukata wajen hada maganin kariya daga cutar a AfriKa ta kudu"

Wannan hadin gwiwwa da kamfanin Swiss Lonza zai samar da wani babban cigaba a fasahar kimiyyar binciken magunguna a kasar, inji Ministar.

Ministar ta kara da cewa, "Ketlaphela zai rage yawan dogaro da magungunan kasashen waje da kasar ke yi kuma zai bada tsaro ga samar da magunguna masu muhimmanci, tsayayyen farashi da ba zai shafi yanayin sauyin kudi sosai ba."

A cikin miliyan 22.9 na al'ummar dake dauke da cutar sida a daukacin nahiyar Afrika, miliyan 5.6 'yan kasar Africa ta kudu ne, a wani rahoton da sashin bada agaji kan cutar sida na MDD ta fitar kwanan nan.

Sai dai kuma mutane miliyan 1.6 ne kawai masu dauke da cutar sidan a kasar Africa ta kudu ke shan maganin hana yaduwar shi inji rahoton. Abin da ya nuna kashi 37 ke nan cikin 100 na wadanda ke karban magani inji Catherine Sozi, wata jami'a mai kula da sashin bada taimako na cutar sida na MDD a Afrika ta Kudu, tace "muna bukatar saka wassu karin miliyan 1.6 cikin masu karbar magani kafin shekara ta 2015" (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China