in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Kenya ta bi sahun sauran kasashen duniya wajen bikin ranar yaki da cutar AIDS ta duniya
2012-12-02 16:27:40 cri
Kasar Kenya ta bi sahun sauran kasashen duniya wajen bikin ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya, tare da yin kira ga dukkan 'yan kasar, da su yi kokarin sanin matsayinsu ko suna dauke da cutar ko A'A, domin ta hake ne kadai za a samu nasarar kawar da cutar.

Mataimakin shugaban kasar Kenya Kalonzo Musyoka wanda ya kaddamar da bikin ranar a garin Nakuru dake kasar ta Kenya, ya bukaci ma'aikatar shirye-shirye na musamman da hukumar kare yaduwar cutar ta kasa da su kirkiro kotun da ta shafi cutar AIDS, irinta ta farko a duniya wadda ta kasance abin misali a fadin duniya.

Musyoka ya ce, manufar wannan kotun ita ce, daukar kwararan matakan da za su kai ga cimma nasarar kawar da rashin nuna wariya ko bambanci ga wadanda ke dauke da cutar, ta hanyar bullo da dokoki da manufofi da za su karfafa kare 'yanci da hakkin bil-Adama.

Kasar ta Kenya da ke gabashin Afirka, tana daya daga cikin kasashen da cutar ta yi wa illa, musamman tsakanin yara, wannan shi ya sa gwamnatin kasar ta bullo da matakin hana yaduwa tare da yiwuwar kamuwa da cutar daga uwa zuwa ga jaririnta.

Taken bikin na wannan shekara shi ne, kawar da cutar kwata-kwata a kasar, hana nuna wariya ga masu dauke da cutar tare da magance wadanda ke mutuwa sanadiyar cutar.

Muskoya ya kuma yi kira ga jama'a, da su yi kyakkyawan amfani da wannan kotu, don tabbatar da cewa, ba a take musu 'yanci ba saboda wai suna dauke da cutar kanjamau.

Yayin da kasar ta yi nasara a yaki da cutar, ta hanyar bullo da dokoki, su kuma jami'ai sun yi kira ga jama'a da su canja halayensu da yadda suke gudanar da rayuwa, ta yadda za a samu nasarar yaki da cutar ta kanjamau.

Ya kuma nanata kudurin gwamnati, na samar da kudaden da ake bukata, matakan da za su yi jagora ga cimma nasarar kawar da wannan matsala. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China