in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Burundi na bukatar dalar Amurka miliyan 349 domin yaki da cutar kanjamau bisa shekaru biyar
2012-06-01 10:56:38 cri
Kasar Burundi ta amince a ranar Alhamis da tsarin dubarar kasa ta yaki da kanjamau bisa lokacin shekarar 2012 zuwa 2016, tsarin na bukatar dalar Amurka miliyan 349. Shirin ya samu amincewa daga majalisar kwamitin kasa na yaki da Sida, a gaban muhimman abokan hulda dake taimakawa kasar ta fuskar kudi da kayayyaki a wannan fanni, ta yadda za'a gaggauta kokarin kasar wajen daukar matakai kan wannan annoba ta VIH/SIDA domin cimma manufar kowa ya samu hanyar yin rigakafi, samun jinya, taimako da samun magani. A cikin sakamako 66 na kayayyaki da manufofin da ake sun samu, akwai batun rage adadin yaduwar wannan cuta daga uwa zuwa dan ta da kashi 2 cikin 100. Adadin da ya kasance da kashi 23 cikin 100 a cewar wani sakamakon bincike a shekarar 2010. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China