in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yara kusan 200,000 na dauke da kwayoyin cutar kanjamau a Mozambique
2012-07-23 14:56:32 cri
A kasar Mozambique, kimanin yara dubu 200 ne suke dauke da kwayoyin cutar Sida kuma akasarinsu, yara ne da iyayensu mata ba su samu taimako na yin rigakafin yaduwar wannan cuta daga uwa zuwa jinjiri ba, a cewar mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Mozambique Nazira Abdula, wanda jaridar Noticias ta rawaito kalamansa.

"Matsala ce mai ta da hankalin gwamnatin kasar da ofishin ministan kiwon lafiya na kasar.'' in ji ministan a yayin wani taro na baya-baya kan rigakafin yaduwar cutar daga uwa zuwa jinjiri, zaman taron da ya samu halartar matar shugaban kasar Portugal Maria Cavaco Silva da kuma matar shugaban kasar Mozambique madam Maria da Luz Guebuza.

Nazira ya amince cewa, kasar Mozambique ba ta cimma wani matsayin a-zo-a-gani ba a cikin aikin yin rigakafin yaduwar cutar HIV daga uwa zuwa jinjiri. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China