A yayin ziyarar, kafofin yada labaru na kasar Amurka irinsu, jaridar "The New York Times" sun rubuta bayani da cewa, a yayin ziyarar farko ta shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi bayan hayewarsa karagar mukami, ya yi sharhi game da burin kasar Sin, da batun tattalin arziki da cinikayya, da dangantakar da ke tsakaninta da manyan kasashen da suke samun bunkasuwa sosai. Bayanin ya ruwaito wani kwararren kasar Sin na cewa, daga cikin kasashen da shugaban Xi ya ziyarta, ana iya gano cewa, kasar Sin na dukufa ka'in da na'in wajen yunkurin raya batun kasa da kasa cikin demokuradiyya, da kokarta sa kaimi ga kafa tsarin dokokin kasa da kasa cikin adalci.(Bako)