Sharhin ya ce, a shekaru 20 da suka gabata, a nahiyar Asiya, musamman a kasar Sin, an samu babban ci gaba a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma, wanda ya taimaka ga samun bunkasuwar tattalin arzikin dukkan duniya. Dandalin tattaunawa na nahiyar Asiya na Boao da kasar Sin ta kafa ya kasance wata muhimmiyar hanya ga kasashen waje wajen fahimtar kasashen Asiya da kuma manufofin kasar Sin a fannin tattalin arziki. A gun dandalin na Bo'ao na bana kuma, an gudanar da taron tattaunawa mai taken "kasashen Afirka masu tarihi za su samu sabon ci gaba", inda shugaban kasar Zambia Michael Sata ya yi wani jawabi na zuburar da kasar Zambia da sauran kasashen Afirka wajen hadin gwiwa tare da kasar Sin da sauran kasashen Asiya. A cewarsa, kasashen Afirka ciki har da kasar Zambia suna fatan koyon fasahohi daga kasashen Asiya ta hanyar dandalin tattaunawar na Asiya wato a Boao don canja matsayinsu na koma baya zuwa matsakaitan kasashe a fannin tattalin arziki a duniya.
Ban da wannan kuma, sharhin ya zargi ra'ayin da wasu mutane ke bayyanawa na cewa wai wasu kasashen Asiya su kan yi ciniki da kasashen Afirka ne domin debe moriyar dake nahiyar kawai. Sharhin ya nuna cewa, wannan ra'ayi ba gaskiya ba ne, domin kasar Sin ta yi alkawarin zuba jari har dala biliyan 20 ga kasashen Afirka da dama, kana ta ce za ta samar da kudi har dala miliyan 750 ga nahiyar Afirka a fannonin aikin gona, da ayyukan more rayuwa tare da bada kudi dala kimanin miliyan 50 domin taimakawa kamfanonin matsakaita da kanana dake nahiyar. Wannan mataki abu ne mai daraja a halin koma bayan bunkasuwar tattalin arziki da ake ciki a duniya. (Zainab)