in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da shugaban majalisar al'ummar kasar Aljeriya
2013-04-08 09:39:05 cri
An yi wata ganawa tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping, da shugaban majalisar al'ummar kasar Aljeriya Abdelkader Bensalah a garin Bo'ao na lardin Hainan a ran 7 ga wata.

Yayin ganawar, Mr Xi ya bayyana cewa, Sin da Aljeriya abokan gumi ne, kuma jama'ar kasar Sin ba zasu manta da muhimmin taimakon da Aljeriya ta baiwa kasar ba, dangane da samarwa Sin matsayinta a MDD, shugaban ya kuma mika godiya a madadin kasarsa,bisa goyon baya da Aljeriya ta nunawa kasar Sin, kan wasu manyan batutuwan da suka shafi moriya mai daraja da kasar Sin ta samu.

Mr Xi ya nanata cewa, Sin na fatan kara hadin gwiwa da yin mu'amala da kasar Aljeriya a dukkanin fannoni, tare kuma da zurfafa dangantakar dake tsakaninsu.

A nasa bangare shugaban majalisar al'ummar kasar Aljeriya Abdelkader Bensalah cewa yayi, Aljeriya na samun taimako daga kasar Sin ko a wajen sha'anin neman samun 'yanci da 'yantar da al'ummar kasar, ko kuma a fannin raya kasa. Haka nan Aljeriya na mai da hankali sosai kan zumunci dake tsakanin kasashen biyu, tana kuma fatan kara mu'amala tsakanin shugabannin kasa da kasa, da habaka cinikayya tsakaninsu, sannan da batun kara hadin gwiwa a fannin zuba jari da dai sauransu, da sa kaimi ga kara samun bunkasuwar dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China