Kamfanin gidan rediyon Birtaniya BBC ya yi bayanin cewa, a yayin ziyarar shugaban Xi, ya daddale yarjejeniyoyi da shugabannin kasashen duniya da dama, kuma ya ba da tabbaci game da inganta dangantakar hadin gwiwa tsakanin bangaren kasar Sin da kasashen Afrika.
A cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin ta zama babbar abokiyar cinikayyar kasashen Afrika. A yayin ziyarar, Shugaban Xi ya bayyana cewa, tasirin bunkasuwar kasar Sin, ta zama wata babbar dama da ba a taba ganin irinta ba ga kasashen Afrika, haka kuma ita ma bunkasuwar kasashen Afrika, ta kawo alfanu ga kasar Sin, sabo da haka, Sin tana fatan yin kokari tare da kasashen Afrika, don yin amfani da wannan dama.
Kafofin yada labaru na kasar Birtaniya kamar jaridar "Financial Times" da ta "Guardian" da "The Daily Telegraph" sun rubuta bayanai da dama, don bayyana halin da ake ciki game da ziyarar shugaban kasar Sin a kasashen waje. (Bako)