Har ila yau, bisa labarin da aka samu daga jaridar mel ta rana-rana ta kasar Zambia, an ce, yayin taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar Boao na Asiya, shugaba Michael Sata ya bayyana cewa, babban jigon taron, wato "neman samun bunkasuwar nahiyar Asiya baki daya, ta hanyoyin yin kirkire-kirkire, da sauke nauyi da kuma yin hadin gwiwa", ya nuna fatan kasashen Asiya sosai, wajen neman bunkasuwa cikin lokutan da suka gabata, da halin da ake ciki, dama nan gaba.
Cikin jawabin nasa, shugaba Sata, ya kuma yi kira ga kasashen Asiya da su kara zuba jari a kasashen Afirka ciki har da kasar Zambia.
A wannan rana, Mr. Sata ya kuma halarci reshen taron dandalin tattaunawa na Boao na "neman bunkasar nahiyar gargajiya ta Afirka", inda ya yabawa babban sakamakon da Sin ta samu cikin 'yan shekarun da suka wuce ta fuskar tattalin arziki, da zamantakewar al'umma, tare da bayyana cewa, dole ne kasashen Afirka su yi koyi da kasar Sin daga fannoni da dama. (Maryam)