A ranar 8 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi hira tare da 'yan kasuwa na gida da waje da dama, da suka halarci taron tattaunawa na Boao da ake yi a lardin Hainan da ke kasar Sin, inda ya jaddada cewa, kasar Sin za ta nace ga manufar yin gyare-gyare a gida, tare da bude kofa ga kasashen waje, haka kuma za ta ci gaba da samar da kyakkyawan yanayi ga masana'antun kasashen waje da ke kasar. Shugaban Xi ya kuma yi fatan masana'antun kasashen waje za su yi amfani da wannan dama, don kara samun ci gaba a kasar.
Bugu da kari kuma, Shugaban Xi Jinping ya ce, Gwamnatin Sin za ta tsaya haikan wajen bin manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, kuma manufofin da kasar Sin za ta bi za su samu kyautatuwa. Ban da wannan kuma, kasar Sin za ta ci gaba da kyautata ayyukan ba da hidima, da kara samar da kyakkyawan yanayi ga masana'antun kasashen waje, domin su samu ikon saka jari, da bude sana'o'insu a kasar Sin, kuma yana fatan 'yan kasuwa na kasashen duniya, za su yi amfani da kyakkyawar damar samun ci gaba kasar Sin, don raya masana'antunsu a cinikin kasar."(Bako)