in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Zambiya
2013-04-06 20:53:42 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Zambiya Michael Sata ranar 6 ga wata a birnin Sanya dake lardin Hainan na kasar Sin, inda shugabannin 2 suka yi musayar ra'ayi kan wasu manyan batutuwan da suka hada da huldar dake tsakanin kasashen nasu, dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, yanayin da nahiyar Afirka ke ciki, da dai makamantansu.

Shugabannin 2 har ila yau, sun nuna cewa suna darajanta zumunci da ya dade a tsakanin kasashen 2, kana za su yi kokarin ci gaban wannan hulda.

A jawabinsa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce, zumuncin dake tsakanin kasashen 2 ya dade kuma yana da zurfi, kana bangarorin 2 suna marawa juna baya wajen kula da batutuwan da suka safi moriyarsu, da taimakawa juna a kokarinsu na raya kasa. Layin dogo da ya hada kasar Tanzaniya da kasar Zambiya, wanda kasar Sin ta ba da taimako wajen gina shi, ya kasance wata babbar shaida wadda ta tunasar da jama'ar kasashen 2 zumuncin dake tsakanin Sin da Zambiya, da kuma Sin da nahiya Afirka.

Abubuwan da suka faru a baya sun tabbatar da cewa, kokarin raya huldar dake tsakanin kasashen Sin da Zambiya ya kawo hakikanin amfani ga jama'ar bangarorin 2, don haka kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan huldar dake tsakanin kasashen 2, kana tana son ci gaba da raya dangantakar don ta dace da zamanin da muke ciki.

Shugaba Xi ya kara da cewa, bai jima ba da gama ziyararsa a kasashen Tanzaniya, Afirka ta Kudu, da jamhuriyar Congo, inda ya gano wani yanayi mai kyau da kasashen Afirka suke ciki wajen kokarin raya kansu tare da tabbatar da zaman lafiya, duk da cewar ba a rasa matsala da kalubale. Don haka, kasar Sin za ta ci gaba da ganin nahiyar Afirka a matsayin aminiya da kawa, da kokarin tabbatar da zaman tsintsiya madaurinki daya a tsakanin kasashen Afirka, da mara ma kasashen baya a kokarinsu na neman zaman lafiya da ci gaba.

A nasa bangare, shugaba Micheal Sata ya bayyana cewa, jama'ar kasar Zambiya suna ma kasar Sin godiya kan yadda kasar ta dade tana baiwa Zambiya taimako wajen gina kasar. A kuma wannan zamanin da ake ciki, kasar Sin, yayin da take kokarin raya kanta, ta samar da kyakkyawar dama ga Zambiya da ma daukacin nahiyar Afirka domin su bunkasa kansu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China