Babban aikin taron shi ne, yin kira ga kasashen duniya, da su ba da taimakon kudi ga yankin Darfur, don cimma burin tattara dallar Amurka a kalla biliyan 7.2 cikin shekaru shida masu zuwa, watau daga shekarar 2013 zuwa ta 2019, ta yadda za a iya bunkasa tattalin arzikinsa, da kyautata zaman rayuwar al'umma, da dai sauran muhimman ayyuka.
Bugu da kari, bisa jadawalin taron, wakilai mahalarta za su tattauna kan yadda za a baiwa yankin goyon baya ta fuskar siyasa da taimakon kudi, kuma za a fitar da wata takardar shirin ba da taimako ga yankin. Haka zalika, wakilan za su yi shawarwari kan batutuwan da suka shafi yunkurin sulhunta yankin, da yanayin mulkin yankin da dai sauransu. (Maryam)