Mista Ladsous ya ce an samu sakamako wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta Doha a yankin Darfur (DDPD). Ya fadi haka a yayin da yake gabatar da rahoto a gaban kwamitin tsaro na MDD inda ya kara da cewa MINUAD na taimakawa shugabannin kabilu daban daban da kungiyoyin fararen hula wajen bunkasa tsarin isar da bayanan da suka shafi yarjejeniyar DDPD a ko ina cikin yankin Darfur.
A cewar shugaban mai kula da ayyukan shimfida zaman lafiya, tawagar MINUAD ta lura da babban cigaban hadin gwiwa da aka samu daga wajen al'ummomin dake sansanonin da aka kebe, daga bangaren jami'iyyun adawa, kungiyoyin fararen hula da kuma hukumomin sassa daban daban .
Saidai kuma yawancin masu bada tallafi na nuna damuwa kan rashin hadin gwiwa game da kundin yarjejeniyar Doha.
Mista Ladsous ya kara da cewa duk da haka ta kamata a kara samar da taimako ga 'yan kasar Sudan don cimma sa hannu kan yarjejeniyar karshe da zata kawo karshen wannan rikici, kuma MDD da kungiyar tarayyar Afrika da sauran wadanda abun ya shafa suna aiki tukuru wajen ganin cewa an aza wata sabuwar hanyar shimfida zaman lafiya mai dorewa a yankin Darfur.
Haka kuma shugaban tawagar MINUAD ya yi Allah wadai da tashe tashen hankalin da aka samu na baya bayan nan yankunan da suka shafi arewaci da yammacin Darfur.(Maman Ada)