Shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir, firayim ministan kasar Katar Sheikh Hamad Bin Khalifa Al-Thani da wasu wakilai kungiyoyin AU, LAS, MDD da na sauran kasashe suka halarci bikin kulla yarjejeniyar.
Firayim ministan kasar Katar Sheikh Hamad Bin Khalifa Al-Thani ya bayyana cewa, yarjejeniyar ita ce shirin tabbatar da zaman lafiya a Darfur, jama'ar Darfur ba su bukatar yakin basasa. Ban da haka kuma, ya yi kira ga bangarori daban daban da su yi kokari tare wajen kyautata zaman rayuwar jama'a a Darfur.(Abubakar)