A yayin bikin, Luo Xiaoguang ya nuna cewa, wannan shi ne karo na uku da gwamnatin kasar Sin take ba da taimakon jin kai ga kasar Sudan, muna fatan jama'ar kasar Sudan za su ci moriyar wannan taimako, ta yadda za'a iyar kara kyautata zaman rayuwarsu, ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasar Sudan, tare da nuna cewa, kasashen biyu za su cigaba da yin hadin gwiwa a wasu fannoni, domin samun moriyar juna.
Jami'in kula da harkokin jin kai na kasar Sudan ya bayyana cewa, wadannan na'urorin aikin noma za su taimaka wa wannan yanki sosai wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma zaman karko, bugu da kari, za su ba da taimako wajen dawowar 'yan gudun hijira gidajensu, tare kuma da samar musu abinci.
Bisa wani labari na daban, an ce, wadannan na'urorin da Sin ta baiwa kasar Sudan sun kai fiye da dubu daya, kamar na'urorin girbi, ban ruwa da dai sauransu. (Maryam)