A gun taron, ministan kula da harkokin waje na kasar Qatar Ahmed Bin Abudulla Al Mahmud ya bayyana cewa, ana aiwatar da yarjejeniyar Doha, amma, ana bukatar bangarori daban daban da su ba da taimakon jin kai, da ba da taimako wajen gina gidajensu.
Kakakin tawagar kasar Sudan Omar Adam Rahman ya bayyana wa manema labaru cewa, gwamnatin Sudan ta tsara taswirar aiwatar da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a Darfur, a sa'i daya kuma, yana fatan kuniyoyi masu adawa da gwamnatin za su sake shiga shawarwarin shimfida zaman lafiya.
Shugaban kungiyar LJM Al-Tigani Al-Sissi ya bayyana cewa, kungiyar tana yin mu'amala tare da kungiyoyi masu adawa da gwamnatin kasar, da yin kira ga wadannan kungiyoyi wajen shiga shawarwarin da gwamnatin kasar Sudan ta shirya, don tabbatar da zaman lafiya a kasar.(Abubakar)