Mahukunta a jihar arewacin Darfur ta kasar Sudan, sun ce, sun samu nasarar shawo kan rikicin kabilancin da ya barke a yankin Al-Siraif, tsakanin kabilun Bani Hussein da Abbala. Rikicin da ya aika da kimanin mutane 53 lahira, baya ga wasu 83 da suka samu raunuka.
A tabakin gwamnan jihar ta arewacin Darfur Osman Yousif Kibir, rundunar hadin gwiwar soji da ragowar jami'an tsaro da aka tura yankin, ta samu nasarar shawo kan al'amarin, bayan da kabilun biyu suka yi dauki ba dadi a ranekun Alhamis da Asabar din da suka gabata.
Bugu da kari, gwamnan ya gargadi al'ummar yankin da su kaurace wa yada jita-jita, da suka iya rura wutar fitina, yana mai cewa, jami'an tsaro za su ci gaba da gudanar da ayyukansu, domin tabbatar da dawowar kyakkyawan yanayin tsaro.
Daga nan sai ya bayyana bakin cikinsa don gane da asarar da ta biyo bayan wannan hatsaniya, yana mai dangata hakan da ayyukan wasu bata gari, dake son fakewa da rikicin domin wawashe dukiyar al'umma. Gwamna Osman Yousif Kibir, ya yi alkawarin aiki kafada-da-kafada da kungiyoyin ba da tallafin jin kai, domin samar da taimako ga wadanda wannan balahira ta aukawa.
Kafin wannan ma dai a cikin watan Janairun da ya gabata, sai da kabilun biyu suka kafsa fada tsakaninsu, kan wata mahakar Zinari ta Jabel-Amer, dake yankin na Al-Siraif, wanda hakan ya sabbaba mutuwar kimanin mutane 100.(Saminu)