in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD ta damu kan halin da yankin Darfur ke ciki
2013-01-10 11:39:52 cri

Mai magana da yawun babban sakataren MDD Mr. Martin Nesirky ya bayyana a yayin taron manema labaru na rana rana da ya ke jagoranta, cewa, ziyarar da mataimakiyar wakilin musamman, kuma mai rike da jagorancin tawagar hadin gwiwar MDD da kungiyar AU ta wanzar da zaman lafiya UNAMID Aichatou Mindaoudou ta kai Zalingei, hedkwatar tsakiyar Dafur a ranar Talata 8 ga wata, ta ba ta damar ganin mawuyacin halin rigingimun da yankin ke fuskanta. Ta kuma samu zarafin tattaunawa da gwamnan tsakiyar Dafur, wanda ya bayyana mata cewa, 'yan tawaye su kwace garuruwan Golo da Rockero dake yammacin Jebel Marra, a ranar Litinin din da ta gabata, lamarin da ya sabbaba iyalai kimanin 850 rasa matsugunnansu. Wannan hali ya sanya Mindaoudou nuna takaicinta ga halin da yankin na tsakiyar Dafur ke ciki, tare da bayyanawa mahukuntan yankin, aniyar tawagarta, ta tabbatar da baiwa mahukuntan taimakon da ya dace, ciki hadda na ayyukan jin kai. Daga nan sai ta yi kira ga dukkanin wadanda ke da ruwa da tsaki kan wannan rikici, da su tabbatar da martaba harkokin bil'adama, kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China