in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na ba da taimako ga wadanda rikicin kabilanci ya shafa a arewacin Dafur
2013-01-17 10:27:28 cri

Mataimakin mai magana da yawun babban sakataren MDD Eduardo Del Buey, ya bayyana cewa, MDD da rundunar samar da zaman lafiya ta majalisar na hadin gwiwa da ragowar masu ruwa da tsaki, wajen ba da agaji ga al'ummomin da rikicin kabilanci dake wakana a arewacin Dafur na kasar Sudan ya ritsa da su. Del Buey ya bayyana hakan ne yayin wani taron ganawa da manema labaru da ya wakana ranar Laraba 16 ga wata, yana mai cewa, rundunar wanzar da zaman lafiya ta kasashen Afirka UNAMID da hadin gwiwar MDD, da ma hukumomin gwamnatin tarayya da na jahohin kasar ta Sudan na mai da hankali ga batun tallafawa fararen hula daga kabilun Beni Hussein da na kabilar Aballa, wadanda rikici, kan ikon mallakar wuraren hakar gwal ya ritsa da su, ko da yake dai rahotannin baya bayan nan na nuna cewa, an tsagaita fada tsakanin bangarorin biyu. Hakan dai ya biyo bayan shiga tsakani da mahukuntan kasar suka yi, wanda hakan ya ba da damar sanya ranar Alhamis 17 ga wata, a matsayin ranar fara taron sulhuntawa tsakanin kabilun.

Don gane da matakan da ake dauka, Del Buey ya ce, UNAMID na shirin fara kaiwa yankunan El-Sereif da Garrah Azawia, tan 75 na kayayyakin bukatun yau da kullum, tun daga ranar Laraba 16 ga wata, za kuma ta bai wa hukumar abinci ta duniya tallafin da ya dace, domin gudanar da aikace-aikacenta a wadannan yankuna.

Fada tsakanin bangarorin biyu dai ya barke ne tun ran 5 ga watan nan a yankin Jebel Amer, ya kuma sabbaba mutuwar fararen hula sama da 100, tare da kone kauyuka, yayin da kuma wasu mutane kimanin 70,000 suka tsere daga gidajensu a yankin mahakan ma'adanai na Jebel Amir. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China