Ziyarar da shugaban kasar Jamus mr. Joachim Gauck zai fara a kasar Sin a ranar 20 zuwa 24 ga watan March, 2016 yana jan hankalina sosai bisa la'akari da tasirin kasashen 2 ta fannin tattalin arzikin duniya da kuma tasirin da kasashen Sin da Jamus suke da shi ta fannin samar da zaman lafiya a dud duniya. Kana kasashen Sin da taraiyar kasar Jamus sun kafa huldar diplomasiya da cinikaiya da musayar al'adu a tsakaninsu a shekarar 1972. Muna fata wannan ziyarar da shugaban Jamhuriyar kasar Jamus mr. Joachim Gauck zai yi a jamhuriyar Jama'ar Sin bisa gaiyatar da shugaban kasar Sin shehun malami Xi Jinping ya yi ma shugaban kasar Jamus za ta kara inganta abokantaka da kuma huldar jakadanci a tsakaninsu zuwa wani saban mataki mai kyau.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.