Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, ina farin cikin shaida muku cewa, yau Jumu'a 26 ga watan Fabrairu na samu zarafin sauraron sabon shirin ku mai farin jini na 'Allah daya gari bamban' wanda malamai Lubabatu Lei da Maman Ada suka gabatar dangane da wakoki masu dogon kari da suka samu karbuwa tsakanin al'ummar jihar Mongolia ta gida.
Hakika wannan shiri ya kayatar matuka, saboda yadda malamai suka yi mana bayani a takaice dangane da yanayin jihar Mongolia ta gida dake da manyan filayen ciyayi. Abin da ya fi bani sha'awa da wakokin masu dogon kari shi ne yadda wakokin suke dauke da sakonni na soyayya, kewar iyalai ko nasara a fagen wasan kokawa. Babu shakka, kamar yadda na saurara cikin shirin, wakoki masu dogon kari na al'ummar jihar Mongolia ta gida suna da dadin ji.
Amma ina son a mikan wata tambaya tawa ga malama Lubabatu Lei, wai shin wata yarinya mai suna Amina da ta rera wata waka mai dadi a shirin Musulma ce? Wato ina son sanin ko akwai al'ummar Musulmi a jihar Mongolia ta gida.
Da fatan za ku ci gaba da kawo mana shirye shirye masu dadi, nishadantarwa da kuma ilimantarwa. Na gode.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners Club
Kanon Dabo, Nigeria