Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Hakika, na yi farin ciki sosai dangane da bani damar shiga gasar ' China Fans' domin na tofa albarkacin baki na dangane da 'taruka biyu' na shekarar bana karkashin jagorancin JKS.
Babu shakka, akwai fa'ida mai yawa wajen gudanar da taron wakilan jami'ar kasa (NPC) da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa (CPPCC) wato 'taruka biyu' a kowacce shekara. Domin wannan muhimmin taro yana ba da damar yin bibiyar manufofin gwamnati da nufin a kwaskware su ko kuma gabatar da sababbin manufofi da za su dace da bukatun al'ummar kasa dake sauyawa a kowanne lokaci.
A halin yanzu, duniya na fuskantar koma bayan tattalin arziki, lamarin da ya kawo jan kafa ga saurin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin. Ina fatan mahalarta wannan muhimmin taro za su yi amfani da wannan dama wajen gabatar da shawarwari masu ma'ana da tasiri domin fuskantar kalubalen irin tafiyar wahainiya da tattalin arzikin duniya ke yi. Wato ina nufin, a daidai lokacin da wakilan jama'a za su tsara shirin bunkasa tattalin arzikin kasa na shekaru biyar karo na 13 (2016 - 2020) ya dace su yi nazari kan sababbin manufofi da za su kara sa kaimi ga bunkasar tattalin arzikin kasar ta Sin daga matsayin yanzu na kasa da kashi 7%. Amma kuma a daidai wannan gaba, ya dace su yi la'akari da batun muhalli, saboda a halin yanzu manyan biranen kasar Sin na fuskantar matsalar gurbatar iska. Wannan kuwa wata babbar barazana ce ga makomar lafiyar al'umma da kuma baki masu yawon shakatawa. Saboda haka, gabatar da shawarwari kan tsara tafiyar da tattalin arziki mai tsafta wanda ba ya gurbata muhalli na da muhimmanci.
Ban da wannan, wani batu daban dake da muhimmanci yayin tsara shirin bunkasa tattalin arzikin kasa na shekaru biyar shi ne batun daidaita kudin shiga, wato ya dace mahalarta taron su yi muhawara sa'an nan su gabatar da shawarwari kan yadda za a daidaita kudin shiga tsakanin al'umma. Wannan yana da muhimmanci sosai wajen cimma burin gwamnati na rage yawan matalauta a duk fadin kasar. Har ila yau, daidaita kudin shiga zai rage kwararar 'yan cirani zuwa manyan birane, lamarin da ka iya rage cunkoson jama'a yadda ya kamata.
Kazalika, yana da muhimmanci wakilan jama'a da masu ba da shawara su tattauna kan matsalar tsaron yanar gizo, domin kutse cikin wayoyin salula da na'urar komfuta ta mutane yana barazana ga makomar wannan fanni. Fiye da Sinawa miliyan 750 suna amfani da yanar gizo ta wayoyin salular su wajen sayen kayayyaki, ko biyan kudaden hidima, dangane da haka ya dace a kara tsaro a wannan bangare. Sauran batutuwan da ya dace mahalarta su tattauna a kai sun hada da daidaita farashin gidaje, inganta harkar kiwon lafiya, da sauransu.
Wani batu mai muhimmancin gaske da wannan taro ya dace ya dorawa fifiko shi ne batun yaki da cin hanci da karbar rashawa, dangane da haka, ya dace mahalarta taron su gabatar da sababbin matakan yaki da karbar toshiyar baki domin dakile wannan matsala dungurungum. A nan ya zama wajibi a jinjina wa shugaba Xi Jinping, wanda ya shiga yaki gadan gadan da masu karbar na goro tun bayan da ya dare kan karagar mulki.
A karshe, ina da ra'ayin cewa duk da koma bayan tattalin arzikin da kasar Sin ke fuskanta, akwai kyakkyawar makoma ga tattalin arzikinta bisa la'akari da cewa matsayin kashi 6.5% na ci gaban tattalin arziki da take kNigeria
lin yanzu wani sakamako ne mai kyau musamman idan an kwatanta da na sauran kasashe masu ci gaba. Ban da wannan, kasar Sin ta yi kokarin kara kyautata huldar ta da kasashe aminanta tare da bayar da tallafi na kudi ko na ababen morewa rayuwa ga kasashe masu tasowa musamman daga nahiyar Afirka.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners Club
Chiromawa Quarters
P.O. Box 1147
Kano State 700001
NigeriaOn