in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sako daga malam Nuraddeen Ibrahim Adam a Kano ta Nijeriya dangane da taruka biyu na kasar Sin
2016-03-01 09:00:01 cri
Zuwa ga sashen Hausa na Rediyon kasar Sin CRI.

Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan dukkanin ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing.

Hakika ina sane da cewa, a kowacce shekara kasar Sin tana gudanar da taron wakilan jama'ar kasa (NPC) da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa (CPPCC) da aka fi sani da 'taruka biyu'. Kuma a koda yaushe wadannan 'taruka biyu' suna jan hankali na saboda muhimman batutuwan fa ake tattaunawa game da shawarwari da ake gabatarwa da kuma zartar da sabbin kudurori.

Babu shakka, taruka biyu na wannan shekara suna da matukar muhimmanci, domin akwai batutuwa da dama wanda ke bukatar a gudanar da shawarwari a Kansu. Misali, idan za mu fara da batutuwan da suka shafi harkokin cikin gida, akwai bukatar wakilan su tafka muhawara kan yadda za a dauki sahihan matakan shawo kan gurbatar iska a manyan biranen kasar Sin da suka hada da Beijing, Shanghai, Hubei, da sauransu. Wannan matsala ba ma kawai tana barazana ne ga lafiyar al'umma ba, har ila yau tana kore baki masu yawan bude ido ko masu son zama a kasar Sin domin gudanar da harkokin kasuwanci ko aiki. Ban da wannan, akwai bukatar mahalarta taron su bullo da sabbin manufofin bunkasa tattalin arziki sakamkon tafiyar wahainiya da tattalin arzikin duniya ke yi. Domin a baya bayan nan, wasu alkaluma sun tabbatar da cewa tattalin arziki kasar Sin ya samu koma baya mafi tsanani cikin shekaru 25.

Sauran batutuwan dake bukatar shawarwari yayin taruka biyu sun hada da batun tazara tsakanin masu iko da talakawa wacce ke kara fadada a kullum. Da batun ingancin abinci ko magunguna, rage kwararar al'umma zuwa biranen, da karfafa yaki da hanci da rashawa da shugaba Xi Jumping ya dauki gabarar aiwatarwa tun bayan da dare kan karagar mulki, da dai sauransu.

Kan batun da ya shafi kasa da kasa kuwa, ya kamata wakilan su bullo da manufofi masu inganci da tasiri kan batun takaddama a tekun kudancin kasar Sin. Haka nan, ya dace wakilan su yi muhawara domin ganin kasar Sin ta zurfafa rawar da take takawa wajen shawo kan rikicin kasar Syria da ke neman ya gwara kawunan manyan kasashen duniya. Lamarin da ka iya zama sanadin fadawa yankin duniya na 3.

Ina fatan za a gudanar da wannan taro lami lafiya kuma za a cimma nasarar dukkanin wasu manufofi da a ka tsara. Na gode.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China