Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake a nan Kano. Yayin da mu ke ban kwana da shekarar 2015 ita kuma sabuwar shekara ta 2016 ta fara kwankwasa kofa, ya dace na gabatar da sakona na musamman dangane da fatan alheri, arziki da zaman lafiya ga daukacin ma'aikatan CRI Hausa. Hakika, duniya ta fuskanci kalubale iri-iri da suka hada da karuwar ayyukan ta'addanci, faduwar farashin danyan mai, koma bayan tattalin arziki, matsalar kwarar 'yan gudun hijira, da sauransu. Ina fatan wannan sabuwar shekara ta 2016 za ta kasance mai tattare da dimbin alheri, arziki da zaman lafiya.
Kazalika, ina so na yi amfani da wannan dama wajen taya dimbin al'ummar Sinawa murnar sabuwar shekara mai alamar biri bisa kalandar gargajiya, da fatan za a gudanar da wannan biki mai muhimmanci ga Sinawa lami lafiya.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria