Kyautar lambar yabo ta Noble prize da aka karrama shahararriyar masaniyar ilmin likitanci yar kasar Sin malama Tu Youyou, abune da ya dace ganin irin kokari da kwazo da ta nuna wajen kirkiro da wani saban nau'in magani mafi inganci na yaki da zazzabin cutar malaria. Babu shakka, bata lambar yabon zai kara bata zarafi da azama ta kara bada himma sosai ga bunciken wani nau'in maganin yaki da cutar zazzabin malaria mai karko makamancin wanda ta kirkiro a halin yanzu.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.