Cike nake da farin ciki a yau, ina kuma fata kuna nan cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
Tun ba yau ba nake hangen kasancewar bunkasar sashen Hausa na CRI, a hankali kuma cikin natsuwa. An ce, 'da sannu giwa ta fi sauran dabbobi girma'.
Kafe sanarwa mai taken, 'Muhimmiyar Sanarwa' a shafinku na yanar gizo yasa na bincika sai naga kuna sanar da mu cewar kun samar da karin wata hanya da mai sauraren ku zai yi amfani da ita wajen tuntubar ku kai tsaye a kowane lokaci. Hakika, wannan sabon tsari da kuka kirkiro na kiran ku ta waya domin aika muku da sako ko aika gaishe-gaishe yana da kyau, kuma wannan hanya zai taimaka sosai wajen kara inganta mu'amala da karfafa dankon zumunci a tsakanin ku da duk kan mai saurare.
Na yi murna da wannan ci gaba da muka samu. Allah Ya kara muku basira.
Naku,
Salisu Muhammad Dawanau,
Abuja, Najeriya.