Ina mai gabatar muku da sakon gaisuwar barka da sabuwar shekara ta 2016 zuwa ga dukkan ma'aikatan sashin Hausa na cri. Agaskiya mu masu sauraronku a jihar Yobe,taraiyar Nigeria mun samu zarafin sada zumunci da ku cri Hausa a cikin shekarar badi ta 2015 kuma kun ba mu babban zarafin samun wayin kai adangane da hakikanin abubuwan dake faruwa a kasar Sin da kuma kasashenmu na Afirka da ma dud duniya baki daya.
Kana kun gabatar mana da shirye-shirye masu inganci a cikin shekarar badi, 2015. Muna fata za ku ci gaba da yin kokari sosai kamar yadda kuka yi a shekarar 2015 da ta gabata, amin.
Daga Malam Ali Buuge kiraji Gashua.