Ina fata kuna lafiya kamar yadda muke a nan birnin Abuja ta Najeriya.
Na rubuta wannan sako ne domin in jinjina muku saboda namijin kokarinku wajen fadakarwa da ilmantarwa a kullum.
A 'yan kwanakin nan da muke ciki, mun saurari shirye-shirye masu sosa rai da kuma kayatarwa musamman masu nasaba da yake-yaken da aka yi shekaru 70 da suka shude tsakanin kasar Sin da Japan, da kuma irin nasarorin da yake-yaken suka haifar.
Hakika, yanayin yaki, wani yanayi ne da ke sanya nadama da yin la'akari domin kauce wa gaba. Mun kuma bi ku a sannu-sannu a yayin shirin gagarumin faretin da dakarun/ sojojin kasar Sin suka gabatar wa Duniya. Wannan abu ya burgeni sosai.
Gaisuwa ta musamman gare ku a sashen Hausa.
Naku,
Salisu Muhammad Dawanau
Abuja, Najeriya